Kamar yadda rahotanni ke cewa mayakan na Boko Haram sun kai harin ne a Muduhu da Nyibango sun kona gidajen mutane da kona abinci,wanda kawo yanzu ba’a da cikakken alkalumman wanda lamarin ya shafa.
Wani da ya tsallake rijiya da baya yace,sun yi shigar burtu ne tamkar yan banga cikin dare wanda nan take sai mayakan na Boko Haram suka soma harbi ba kakkautawa da kuma kone kone.
Hukumomin tsaro dai a jihar Adamawa basu ce komi ba kawo yanzu,to sai dai kuma shugaban karamar hukumar Madagalin Yusuf Muhammad ya tabbatar da wannan sabon hari inda yace abun takaici ne abubuwan dake faruwa a yanzu.
Kamar dai shugaban karamar hukumar,shima dan majalisar wakilai dake wakiltar yankin Michika da Madagalin,Mr Adamu Kamale ya tabbatar da aukuwan lamarin inda ma ko ya musanta batun cewa babu sauran yan Boko Haram a wadannan yankunan Michika da Madagali da aka kwato dake kusa da dajin Sambisa.
Wata matsalar da ake fama da ita ma yanzu ita ce na yadda jami’an sojin dake aiki a wajen ba sa karkashin rundunan soji ta 23 dake Yola ko na Mubi, wato suna karkashin na Chibok dake jihar Borno,da hakan kan zama kandagarki ga jami’an gwamnatin jihar kamar yadda shugaban karamar hukumar Madagalin ya bayyana.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5