An kai harin ne da sanyin safiyar yau Juma’a bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa, sannan wasu ‘yan bindiga suka yi arangama da wasu dakarun kasar Kenya da aka jibge a sansanin.
Kungiyar ta Al shabab dai ta yi ikrarin ta kashe da yawa daga cikin dakarun, kuma ta karbe ikon sansanin, sai dai rundunar hadin gwiwar, wacce ake wa lakabi da AMISOM, ba ta tabbatar da wannan ikrari ba.
Amma wasu mazauna yankin sun ce lallai mayakan na Al shabab sun karbe ikon garin sannan sun daga tutarsu, yayin da suka kuma ce mayakan sun karbe wasu makamai a cikin wata mota mallakar dakarun hadin gwiwar.
Ko a watannin Yuni da Satumbar shekarar da ta gabata ma, mayakan na Al Shabab sun kai wani hari makamancin wannan, inda suka halaka da dama daga cikin dakarun hadin gwiwar na AMISOM.