An dai kwashe tsawon lokaci cikin rana da dare ana gudanar da addu’oi da kuma zikira a taron.
A jawabin da ya gabatar, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya jagoranci taron maudlin ya ce maksudin hada taron shi ne Allah ya ce a gode mai idan ya baiwa mutum ni’ima.
“Babbar ni’ima da Allah ya kawo mana a duniya babu kamar zuwan Annabi Muhammad salallahu alaihi wasallam, saboda haka muke taron mauludi, kuma bayansa a duniya, zuwan Shehu Tijjani ya amfane mu a duniya, ya sa muna yin istigfari da yawa, ya sa mun yiwa Annabi salati da yawa da la’ilaha ilallah ta hanyar darikarsa.” In ji Sheikh Dahiru Bauchi.
Ya kuma kara da cewa wannan taron mauludi ba na Bauchi ba ne kadai domin ya kunshi mutane da dama daga sassan nahiyar Afrika.
“Ai wannan taro ba na Bauchi ko Najeriya ne kadai ba, muna sauraron baki daga Morocco da Senegal da Algeria da Misra da kasashe na kusa-kusa.” Ya kara da cewa.
Wasu ‘yan cikin gida da suka halarci taron sun bayyana cewa jahar ta Bauchi an san ta da karbar baki da kuma gudanar da wannan taro.
“Wannan taron mauludi ya koya mana yadda za mu karbi baki, wasu ma baka san su ba, za su zo, su baje kayansu a kofar gidanka.” In ji wani mazaunin garin na Bauchi.
Ga karin bayani a rahoton wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5