Matukar Damuwa Game Da Rashin Lafiyar Aleksey Navalny

The White House

Kasar Amurka na ci gaba da nuna damuwa game da kara galabaita a lafiyar dan adawa da yake tsare na Rasha, Aleksey Navalny. Shugaban adawar ya kawo karshen yajin cin abinci na kwanaki 24 a kokarin tilasta wa hukumomin gidan yari da su ba shi kulawar da ta dace game da tsananin ciwon da ke bayansa da kafafunsa. Navalny ya kuma ce yana fama da wani mummunan tari da zazzabi sannan kuma an ce an kwantar da wasu da ke kurkukunsa a asibiti saboda tarin fuka.

Shugaba Joe Biden ya nuna damuwa "game da tabarbarewar yanayin Navalny, in ji sakatariyar yada labarai ta Fadar White House Jen Psaki.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ned Price ya sake nanata wadannan damuwa: “Muna kira ga hukumomi da su dauki duk matakan da suka dace don tabbatar da lafiyarsa da kuma tabbatar da lafiyar jikinsa. Kuma muna sake nanata kiran da a sake shi ba tare da bata lokaci ba tare da kawo karshen muzgunawar da ake yi wa magoya bayansa. ”

A ranar 2 ga Maris, dangane da amfani da makami masu guba da Rasha ta yi kan Mista Navalny, Ma'aikatar Harkokin Waje ta fadada takunkumin da ke akwai da aka fara kakaba wa Rasha bayan harin da ta kai wa Sergei Skripal a shekara ta 2018 a Burtaniyya.

Bugu da kari, Ma’aikatar Baitulmali da Ma’aikatar Harkokin Waje sun sanya takunkumi ga wasu mutanen Rasha da cibiyoyin da ke hade da shirin makamai masu guba na Tarayyar Rasha da bangarorin tsaro da na leken asiri. An kuma sanya Rasha cikin jerin kasashen da ke karkashin “manufofin kin amincewa da fitar da kayayyakin tsaro.

“Gwamnatin Amurka ta yi amfani da ikonta wajen aikewa da sako karara cewa, amfani da makamai masu guba da Rasha ke yi da kuma cin zarafin‘ yancin bil adam na da mummunan sakamako. Duk wani amfani da makami mai guba abu ne da ba za a yarda da shi ba kuma ya saba wa ka’idojin kasa da kasa, ”a cewar Sakatare Antony Blinken.

Mai magana da yawu Price, ya yi gargadin cewa "Ba zan so in hango abin da zai iyabiyobaya ba nan gaba ba idan Moscow ta ci gaba ta wannan hanyar." “Kada Moscow ta yi tunanin cewa ba zamu dora mata alhaki ba” sabodagallazawa Mr. Navalny.