Wata babbar jami’ar diplomasiyyar kungiyar tarayyar turai ta ce ‘yan majalisun dokokin Amurka, na da niyyar ganin sun tabbatar cewa tsare-tsaren gwamnatin shugaba Donald Trump kan matsayar da aka cimma da Iran game da shirinta na makamin nukiliyanta a shekarar 2015, ba su shafi matsayar ba, duk da cewa Trump na nuna shakku kan shirin.
“Akwai kwararan alamu da ke nuna cewa manufar ita ce Amurka ta ci gaba da kasancewa a cikin shirin.” In ji jami’ar harkokin wajen kungiyar EU, Frederica Mogherini, yayin wani taron manema labarai da ta gabatar, bayan da ta gana da mambobin majalisar dokokin na Amurka.
Yayin wannan ziyara ta kwanaki biyu da ta kawo a nan Washington, domin tattaunawa da ‘yan majalisun kan huldodin kasuwanci da na tsaro da ke tsakanin tarayyar turai da Amurka, Moghrini ta jaddada irin muhimmancin da kungiyar ta tarayyar turai ta dora kan matsayar da aka cimma da Iran.
Wannan ziyarar ta Moghrini, na zuwa ne a wani lokaci da aka shiga tsaka-mai-wuya kan shirin na Iran, bayan da shugaba Trump ya ki amince da shi domin a cewar shi, Iran ta fi cin gajiyar wannan yarjejeniya.