Matsayin Majalisar Dattawan Najeriya Kan Gyaran Kudurin Dokar Fansho

Pencom

Bayan sauraren kokekoken tsoffin ma'aikata da suka aje aiki akan yadda suke samun matsala wajen karban hakkokin su, Majalisar Dattawa ta sha alwashin yin gyaran kudurin dokar fansho ta kasa domin anfanàr jami'an da suka aje aiki a kasa baki daya. 

Shugaban kwamatin kula da fansho da aikin gwamnati da walwalar ma'aikata na majalisar dattawa Ibrahim Shekarau ne ya bayyana hujjojin yin haka.

Daya cikin hukumomin gwamnati da wannan komitin kula da fansho ke sa ido akai ita ce rundunar 'yansanda, kuma ita ce hukumar da ke jagorantar jami'an tsaro a Najeriya wace ta ke da kimanin ma'aikata dubu 371, 800.

Akwai wadanda suka aje aiki daga hukumar yansanda wadanda ke korafi akan yawan kudin da ake basu a matsayin hakkin yi wa kasa hidima har na tsawon shekaru 35.

Abubakar Abdullahi Dashe tsohon dan sanda ne, ya kuma ce ya aje aiki a matsayin mai anini uku a aikin dan sanda amma Naira dubu 30 ake biyan shi a wata.

Dashe ya ce akwai abin dubawa domin wannan kudi sun yi kadan idan an kwatanta shi da na wasu hukumomin tsaro a kasar. Dashe ya yi kira da a gaugauta duba dokar fansho ta kasa.

Shugaban kwamitin kula da fansho da aikin gwamnati da walwalar ma'aikata Sanata Ibrahim Shekarau ya yi karin haske kan matakin da majalisar dattawa za ta dauka inda ya ce tunda aka yi gyaran dokar fansho a shekara 2014, gwamnati ba ta fara bada kashi 10 cikin dari na fanshon ma'aikata ba, har yanzu kashi 7 ne ta ke biya.

Shekarau ya ce gwamnati ta yi hobbasa na ganin an biya gibin, inda gwamnati ta bada kudi Naira biliyan 130 na biyan gibin da ya taru a baya.

Majalisar dattawa ta sha alwashin sake gyara dokar fansho domin kyautata wa ma'aikata da suka aje aiki bayan kammala wa'adin lokacin aiki da aka dibar masu.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Za Ta Yi Gyaran Kudurin Dokar Fansho Domin Anfanàr Da Jami'an Da Suka Ajiye Aiki