Matsalar Tsaro Ta Shafi Harkokin Zabe A Wasu Yankunan Jihar Rivers

Ga dukan alamu, harkokin tsaro a jihar Rivers na neman rikitar da harkokin zabe a yankin da kuma sakamakon sa, sanadiyyar kashe-kashe da jikkata mutane da dama da wasu ‘yan bangar siyasa suka yi, abinda ya kara munana harkokin tsaro.

Wasu rahotanni sun nuna cewa sojoji sun kusa karbe harkokin tsaro a yankin na jihar Rivers, ko da yake alkaluman da hukumomi ke bayyanawa na wadanda suka mutu basu wuce mutane 9 ba, wasu da suka shaida lamarin sun ce wadanda suka mutu zasu kai akalla mutane 40.

Wani mazaunin yankin da ya so a sakaya sunan sa, ya ce an yi zabe amma ya bar baya da kura. A wasu wuraren ma ba a yi zaben ba sakamakon musayar wutar da ta aka yi tsakanin sojoji da wasu ‘yan bindiga. Ya kuma tabbatar da cewa wadanda suka mutu sun kai talatin da wani abu.

Kawo yanzu dai bayanai sun tabbatar da cewa jama’a tare da iyalan su na ci gaba da yin kaura daga wadannan sassan dake fama da matsalar tsaro a jihar Rivers, kamar irin su karamar hukumar Bonny, da kuma yankin Ogoni. Bayan haka kuma mutane da dama na zargin cewa rundunonin tsaro sun gaza.

Wata mata da ta bayyana sunan ta a matsayin Juliet Jack daga garin Abonnema, ta ce har da jami'in soja cikin wadanda aka kashe kuma an baza sojoji yanzu haka a cikin garin abinda ya tadawa jama’a hankali sosai, ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta janye sojoji daga wannan yankin don a sami zaman lafiya.

Mr. Nnamdi Imoni, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, ya ce sun iya kwantar da kurar da ta tashi kuma an sami wadanda suka yi yinkurin sace akwatin zabe abin da ya yi sanadiyar mutuwar wani soja.

Duk da cewa ba a kammala kirga sakamakon zaben jihar ba a lokacin wannan rahoton, mai magana da yawun hukumar zaben jihar Rivers, Mr. Iduwan Inobo ya ce kimanin kananan hukumomi 9 ne za a sake gudanar da zabe sakamakon rikicin da ya barke a yankunan.

Haka zalika a jihar Akwa Ibom, a yankin na Niger Delta, bayanai na cewa jami’an tsaro na can na sintiri na ko ta kwana, ganin yadda bangarori biyu na jihar ke ci gaba da jayayya akan sakamakon zabe

Ga karin bayani cikin sauti daga Lamido Abubakar Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Tsaro Ta Shafi Harkokin Zabe A Wasu Yankunan Jihar Rivers - 4'15"