Bayan taron Muryar Amurka ta zanta da wasu shugabannin kungiyoyin da suka halarci taron domin karin bayanai.
Ishaq Adamu shugaban wata kungiyar sa kai ta jihar Bauchi yace sun kawo bayanai da dama akan masu satar mutane sun garkuwa dasu domin samun kudin fansa. Yace mutanensa sun kama wasu dake satar mutane aka kaisu wurin 'yansanda amma daga bisani aka sakesu. Yace yanzu sun rasa mutane ukku cikin nasu mutanen.
Ya cigaba da cewa gwamnati ta biya 'yansanda amma bata biya mutanensa ba. Ya yi musali da sarkin Fulanin Duguri wanda ya kama wasu amma da aka sakesu sai suka juya suka kone gidansa. Haka ma a Ningi inda aka kama wasu barayin mutane tare da bindigogi amma bayan sati daya 'yansanda suka sakesu.
Shi ma wani bai bada bayanan asiri kan masu satar mutane ya bayyana tsoro da fargaba dangane da rashin samun kariya da kuma munafuncin abokan aiki. Yace idan an kama yara aka gaya masu wanda ya sa aa masu da zara an sakesu sai su je su kashe mutumin din. Yace akwai kuma wadanda suke aiki tare amma suna tseguntawa yaran. Idan an kama yara a kan sakesu kai kuma da ka kamasu ka rasa inda zaka sa kanka.
Wani mai sarautar gargajiya a garin Bauchi ya roki gwamnati ta ba shugabannin anguwanni ikon mallakar littafin bayani akan kowa da yake anguwarsu. Ya kara da cewa idan jami'an tsaro basu bada kariya ba to masu kawo bayanan siri zasu ji tsoron kawo duk wani bayani na siri.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5