Masu gidajen abinci suna kokawa a jihar Taraba saboda koda ma sun yi wasu abincin kamar tuwon shinkafa mutane ba sa iya saye domin abun da kudinsu zai saya ba zai kosar dasu ba.
Yanzu tuwon masara mutane ke saya maimakon tuwon shinkafa musamman a birnin Jalingo babban birnin jihar Taraba. Masu yin tuwon shinkafa sun daina saboda tsadar shinkafa kuma mutane ba zasu saya ba,
A kasuwar Jalingo ana sayar da shinkafa tiya guda akan nera dari takwas da hamsin yayinda a wasu wuraren ma tsadar ta fi haka. Buhun shinkafa 'yar kasar waje nera dubu ishirin ake sayar da ita.
Kodayake an soma samun sabbin kayan abinci daga manoma amma wasu 'yan baranda suna bi suna sayewa su boye.
Alhaji Ahmed Tukur Jada daya daga cikin shugabannin manoma a jihar Adamawa yana ganin dole ne gwamnatocin jihohi su shigo cikin lamarin su tallafa. 'Yan baranda har gida suke bi suna saye abincin saboda haka dole gwamnati ta bada tallafi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5