Bayanai na nuni da cewa hukumomin yankin suna zargin baki ‘yan gudun hijra da kawo wannan mummunar dabi’a wacce suka ce ta na gurbatar da tarbiya.
Hukumomin a yankin sun ce baya ga shigar baki, tilastawa mata auren wadanda ba sa kauna na daga cikin dalilan da suke jefa ‘yan mata harkar shaye-shaye.
Sannan maraici a cewar kwararru na daga cikin ababan dake haddasa wannan larura.
Amma kamar yadda masana lafiyar jiki suka nuna wannan dabi’a na haifar da matsaloli da dama.
Masu lura da al’amura sun ce akwai bukatar iyaye da masu fada a ji sui do kan wannan matsala domin a samu hanyar da za a dakile ta.
Domin sauraren irin illar wannan matsala ta shaye-shaye da kuma yadda masu harkar ta shaye-shaye suka tsinci kansu a cikin wannan harka saurari rahoton Haruna Mamane Bako daga Nijar:
Your browser doesn’t support HTML5