Rahotanni na cewa yanzu haka a Najeriya, matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi sai kara habaka ta keyi, musamman a arewacin kasar kuma a wurin matasa, yayin da a bangare guda kuma jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin ta NDLEA, take fuskanci turjiya daga masu ta’ammali da kwayoyin, lamarin da kan jawo fito-na-fito a wasu lokuta.
Wannan batu yanzu haka na kara tada hankulan iyaye ganin cewa har da mata a harkar sha da fataucin kwayar.
Alal misali a jihohin Adamawa da Taraba, har kungiyoyi irin wadannan matasa ke kafawa, kuma masu ta’ammali da kwayan sun hada har da mata, kamar yadda wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz ya tarar a wata matattarar yan jagaliya da da yiwa shigan burtu.
Shima Mr Yakubu Kibo dake zama kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Adamawa ya tabbatar da cewa mata sun tsundumma dumu-dumu cikin wannan dabi’ar ta shaye-shaye.
To sai dai kuma ganin yadda wannan matsala ke kara ta’azzara ne yasa wasu kungiyoyi yunkurowa domin fadakar da al’umma game da illar dake akwaia cikinta.Mr Shehu Yohanna, wanda jigo ne a majalisar matasan Najeriya ta NYCN, ya ce abun takaici ne abubuwan dake faruwa.
Manazarta na ganin dole a hada hannu domin yakar wannan matsala ta shan kwaya da matasa ke yi. Shekarau Yerima, wani dan jarida a Yola, ya ce su ma kafafen yada labarai dole su tashi tsaye.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5