Matsalar Satar Jama'a a Wasu Sassan Arewacin Najeriya Na Kara Ta'azzara

A Najeriya, matsalar satar jama’a da kuma ‘yan bindiga masu harbin kan mai uwa da wabi na kara ta’azzara a wasu sassan kasar a yayinda babban zabe a kasar ke karatowa.

Kama daga jihar Zamfara da kananan hukumomin Batsari, da Safana dake jihar Katsina, da yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna, da kuma jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya, dubban jama’a ne ke zama cikin yanayin zullumi a sakamakon ta’addancin wadannan ‘yan bindigar.

Alhaji Ma’aru Ma’undu, na daya daga cikin wadanda suka tsallaka rijiya da baya a yankin karamar hukumar Mariga bayan da aka hallaka ‘yan uwansa guda biyu. Ya bayyana cewa suna zaune kawai sai ‘yan bindigar suka zo a guje suka bude masu wuta daga nan suka gudu.

Shugaban karamar hukumar Rafi a jihar Niger, kuma shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya, Alhaji Gambo Tanko, ya tabbatar da cewa suna fuskantar wannan matsalar a yankin amma suna daukar mataki.

Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta ce tana kokarin fatattakar wadannan miyagun, a ta bakin kakakin rundunar jihar DSP, Abubakar Dan Inna.

Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, a wani yakin neman zabe da ya je karamar hukumar Rafi mai fama da wannan matsalar, ya ce su na ci gaba da daukar matakai don ganin an sami tsaro a wannan yankin.

Ga karin bayani cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Satar Jama'a a Wasu Sassan Arewacin Najeriya Na Kara Ta'azzara - 2'41"

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Satar Jama'a a Wasu Sassan Arewacin Najeriya Na Kara Ta'azzara - 2'41"