Wasu da ba'a sani ba sun sace Injiniya Wilson Gundiri dan shekara 65, tsohon ma'aikacin jami'ar kimiya da fasaha ta tarayya dake Yola kuma wan Injiniya Marcus Gundiri wanda ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam'iyyar SDP.
Alfari Wilson Gundiri babban dan Injiniya Wilson Gundiri ya yiwa Muryar Amurka bayanin yadda aka sace mahaifin nasa. Yace mahaifin nasa yana cikin gonarsa ne a Bole cikin karamar hukumar Yola ta Kudu lokacin da wasu 'yan bindiga hudu suka kamashi suka kuma tilasta masa shiga motarsa kana suka tafi dashi. Alfari yace bai yi tunanin wani dalili ba da zai sa a sace mahaifin nasa.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yansandan jihar DSP Othman Abubakar yace kawo lokacin da Muryar Amurka ta kirashi bai samu labarin sace Injiniya Gundiri ba. Amma dansa yace sun shaidawa 'yansanda kuma har sun gano motar shi Injiniya Gundiri a dajin Bole lokacin da suka bi sawun wadanda suka saceshi.
Yayinda 'yansandan suka hango motar a daji sai mutanen suka gudu da Injiniya Gundiri amma sun bar motar baya.
Sace Injiniya Gundiri shi ne na biyu a jihar cikin 'yan kwanakin nan. Can baya an sace kanin Nuhu Ribadu dan takarar jama'iyyar PDP a jihar.
Ga rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5