Matsalar Rashin Tsaro Na Kara Muni A Gabashin Sokoto

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Alamu na nuna cewa sai mahukumta sun yi da gaske kafin a samu shawo kan matsalar rashin tsaro dake addabar arewacin Najeriya musamman arewa maso yamma.

A daidai lokacin da aka samu saukin matsalar rashin tasro a kananan hukumomin Sabon Birni da Issa a gabashin Sokoto sai ga wata matsala ta satar mutane don neman kudin fansa da satar dabbobi a karamar mulkin Illela da kuma kisar dauki dai dai a karamar hukuma ta Raba.

Karamar humukar Illela da take kan iyakar Najeriya da Nijer, tana fuskantar matsalolin tsaro daban daban duk da yake an girke jami'an tsaro da suka hada da na hukumar hana fasa kwauri, sojoji, jami’an kula da shige da ficen baki da ‘yan sanda da sauran su.

Matsalolin tsaro da ake fuskanta a wannan yankin sun kuma hada da matsalar satar mutane da ta yi kamari a yankin.

Bello Isa Ambarura, dan majalisa mai wakiltan yankin a majalisar dokoki ta jihar Sokoto, ya ce gwamnatin jihar da ta tarayya suna iya kokarin su domin tabbatar da tsaro a yankin gabashin Sokoto, amma dai matsalar satar mutane tana addabar yankin na Illela. Ya ce babu rana da ba a samun labarin kai hari a kan mazauna yanki.

Ambarura ya ce dole ne su koka domin a kawo musu dauki a kan wannan batu, a don haka ya yi kira ga gwamnati ta kawo ma yankin gudunmuwa don al’ummar wurin su samu kwanciyar hankali.

Wadansu mazauna yankin da suka zanta da Muryar Amurka a kan hali da suke ciki a yankin na gabashin Sokoto sun bayyana cewa, mutanen yankin na bukatar daukin gaggawa. Ya kuma ce mutane na jin tsoron zuwa gona da wasu muhimman wurare domin gudun kada a sace su a nemi kudin fansa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce tana sane da abin da ke faruwa yankin kuma tana daukan matakan magance wannan matsala, kamar yanda kakakin rundunar ASP Mahamman Sadik Abubakar ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti

Your browser doesn’t support HTML5

RASHIN TSARO NA KARA MUNI A SOKOTO