Son sake tsayawar shugaba Jonathan takar shugaban kasa ita ce matsalar PDP
WASHINGTON, DC —
Bamanga Tukur ba shi ne matsalar PDP ba son sake tsayawar shugaba Jonathan zaben 2015 shi ne matsalar.
Honorable Abdulrazak Nuhu Zaki dan majalisar wakilai daga jihar Bauchi ya ce mutum kamar Gulak wanda ko zaben unguwarsu bai ci ba wai shi ne yake ba shugaban kasa shawara kan yadda zai ci zabe. Ya ce yanzu gwamnoni biyar sun bar PDP wasu kuma 'yan majalisar wakilai su 37 sun canza sheka kana wasu ma na shirin barin jam'iyyar kuma irin su Gulak suna cewa babu abun da ya samu jam'iyyar ta PDP. Wannan ba gaskiya ba ne domin irin su Nuhu Zaki sun damu. Duk dan PDP mai hankali ya kamata lamarin ya zama abun damuwa a wurinsa.
Yakamata a gane cewa shi Jonathan ba zai dawama ba. Dole wata rana ya bar jam'iyyar. Nuhu Zaki ya ce dalilin da ya sa shi ya dage cikin jam'iyyar tun farko yana cikinta. Nan ya saba. Burinsa shi ne ya bada gudummawa a gyara abun da aka ce ya baci. Idan kuma nufin Allah ne da sauran shan ruwansu a siyasance sai a gyarata.
Koda za'a nitse a jam'iyyar PDP Nuhu Zaki ya ce yana cikinta kuma da yaddar Allah da hakan za'a cigaba da tafiya. Amma abun da ya ke son iyayen jam'iyyar su sani shi ne idan basu tashi tsaye ba sun toshe barakar dake cikin jam'iyyar to ko zata nitse. Ya kirawo shugaban kasa da sauran shugabannin jam'iyyar su fitar da son zuciya su ceto jam'iyyar daga nitsewa amma irinsa sai sun ga abun da ya turewa buzu nadi. A jihar Bauchi suna tare da gwamnansu kuma basa fata a ce har ransa ya baci ya bar jam'iyyar.
Daga karshe Nuhu Zaki ya ce hanya mafi sauki da PDP zata koma ta ci zabe cikin ruwan sanyi kuma da yaddar Allah shi ne shugaba Jonathan ya yi hakuri da tsayawa zaben 2015. Ya duba duk cikin arewa ya zabo wanda ya fi yadda da shi ya mara masa baya ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2015. Idan ya yi hakan an gama magana. Duk buga-bugan da ake yi ba domin Bamanga Tukur ba ne domin Jonathan ne. Domin haka yakamata Jonathan ya yi abun da aka yi masa a shekarar 2011 har ya zama shugaban kasa. Ya manta da sake tsayawa zabe. Ya nemi dan arewan da ya yadda da shi ya tsayarda shi. Idan ya yi hakan duk jam'iyyun da suka taru wuri daya PDP zata bugesu.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5