Matsalar Muhalli A Jami’ar Ahmadu Bello Ta Zaria

Dalibai Masu zanga zanga a Jami'ar Calabar 12, ga Oktoba 2015

Matsalar karancin wuraren kwana matsalace da ta addabi jami’o’I da manyan makarantun kwana a fadin Najeriya, kuma yanzu haka daliban jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria na fama da wannan matsala.

Muryar Amurka ta tattauna da wasu dalibai kan wannan matsala, daliban dai sun hada da Musa Gurama Mohammed da Sa’adatu Adamu da Asiya Abdullahi Indagana da Lukuman Musa da kuma Muhammed Bello, dukkan su dalibai a jami’ar Ahmadu Bello. Sunyi kira ga wadanda abun ya shafa.

A karin bayani da yake kan halin zaman su a Jami’ar ABU, Lukuman Musa, yace a jami’ar akwai guraren kwana har biyu babba da karami inda a babban ne ake samun matsala kasancewar akwai cinkoso .

Ita kuwa Sa’adatu cewa tayi idan aka duba yadda yawan masu karatu a wannan zamanin sunfi yawan dalibai na baya saboda yanzu mutane sun san muhimmancin karatu. Ta kuma yi kira ga gwamnatin Tarayya da gwamnatin jiha domin su hada hannu wajen samun yadda za a kara gina muhalli da zai iya daukar yawancin dalibai.

Saurari hirar Yusif Harande da daliban jami’ar ABU.