Matsalar Mai Ya sake Kunno Kai a Wasu Birane A Najeriya

  • Ladan Ayawa

Cars que to buy fuel in Abuja, Nigeria, Tuesday, Nov. 30, 2010. A strike by Nigerian gas tanker drivers is creating long lines at gas stations in Africa's top oil producer and crippling activity in its cities. Igwe Achese, chairman of the Nigeria Union o

Karancin man fetur naci gaba da kunno kai a birnin Abuja, inda ake ganin dogayen layuka a gidajen mai, dake ciki da wajen birnin

Wakilin sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya ziyarci wasu gidajen mai kuma ya tattauna da wadanda ya taras a cikin wadannan dogayn layukan a gidan man NNPC dake kan titin Murtala Mohammed.

‘’Sunana Al-Amin Mohammed nayi mamaki don jiya na taso daga Gombe na dawo nan Abuja ban sayi mai a hanya ba, domin tunanin akwai mai cikin gari amma yanzu da nazo zan tafi aiki sai naga dogayen layuka duk gidan man dana gitta ba mai, ni kuma banda mai din.Don da dare na dawo kuma nagaji, abinda ban mamaki nan nasha mai kafin na tafi ba kowa cikin gidan mai, amma yanzu dana shigo sai ga dogayen layi’’

Shima wannan dan talikin ga abinda ya shaida wa Hassan din.

‘’Sunana Aminu Dan Mai Ali Yawuri wallahi matsalar mai da muke fama dashi garin Abuja abin sai dai muce Inna Lillahi Wainna Alaihin rajiuna domin bai kamata ace ana matsalar mai cikin garin Abuja ba.’’

Da kuma Hassan ya tambaye shi ko yaya wannan karancin man ke shafar rayuwar su yau da kullun sai yace.

‘’Wallahi yana shafuwar harkokin mu nay au da kullun Tsakani da ALLAH saboda gashi yanzu muna son muje wajen neman abinda zamu ci amma gashi wannan matsalar an ya kawomuna cikas’’

Har ila yau Hassan din ya tattauna da editan jaridar leadership dake fitowa ranar juma’a kuma ga abinda yake cewa game da wannan karancin man fetur din.

‘’ Akwai wadanda suke cewa akwai wadanda ke zagon kasa a wannan gwamnati, akwai kuma wadanda suke gani cewa shi wannan matsala, matsala ne wanda gwamnati ta gagara ta samo bakin zare, to duk dai ko wannene a zamanin nan da kowa yanzu yake cikin wahala amma kuma ana baiwa gwamnatin uzuri yakamata gwamnatin taga cewa wannan lamarin an samu saukin sa.’’

Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Mai Ya sake Kunno Kai a Wasu Birane A Najeriya 3'15