Matsalar karancin man fetur ta soma dawowa wasu sassan arewacin Najeriya, inda ake ganin dogayen layuka a wuraren da ake da dan man. Wakilnmu a Minna Mustapah Nasiru Batsari y ace tun a farkon makon jiya aka wayi gari babu man a galibin tasoshin man da ke arewacin Najeriya.
Mustapha y ace a Minna, babban birnin jahar ta Naija babu karancin man, to amma akwai matsalar a wasu sassan jahar. Wani mai suna Umar Adam Faruk daga Kwantagora ya shaida ma Mustapha ta waya cewa akasarin gidajen mai sun rufe inbanda Total da NNPC. Shi ma wani mai suna Alhaji Aliyu Isa daga wani sashin jahar y ace bas u da man. Don haka Mustapha ya tuntubi Shugaban kungiyar Dillalan man fetur a Najeriya Alhaji Abubakar Maigandi Dakingari, wanda ya tabbatar rashin man a wasu gidajen man, al’amarin da ya alakanta da rashin man a wuraren da ake zuwa dauko – ciki har da Lagos da wasu depot-depot. Bugu da kari, in ji shi, kungiyarsu ta umurci mambobinta cewa kar su sai da mai saboda za su fadi kan farashin da gwamnati ta umurce su su sayar, wato kan Naira 87, alhalin kuwa, sabanin cewa da gwamnati ta yi a rika sai da masu man kan Naira 77 da sulai 6; ana saida masu shi ne akan Naira 82. Wannan, in ji shi, ya sa ‘yan kasuwa da dama sun ji tsoron sayo man saboda gudun faduwa.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5