Me Ke Haddasa Karancin Jini A Asibitocin Nijar?

Ana diban jini daga jikin mutum

Karancin jini a asibitocin Nijar na haddasa asarar rayuka musamman ga mata idan sun zo haihuwa, lamarin da ya sa aka yi nazarin hanyoyin da zasu inganta samun jini daga jama'a bayan an bukacesu.

A asibitocin Nijar, samun jini a lokacin da ake bukatarsa domin taimakawa wadanda yake cikin matsala na da wuya.

Matsalar samun jini ya sa hukumomin kiwon lafiya suka taru wuri guda domin nazarin hanyoyin da za a fitowa matsalar.

Asibitocin da ke karbar haihuwa su ne suka fi fuskantar matsalar kamar yadda Lawali Ali shugaban asibitin haihuwa d ake birnin Yamai ya bayyana. Ya ce kwanaki biyu da suka wuce wata mata da ta zo haihuwa tana bukatar jini amma ba ta samu ba. Likitoci fiye da ashirin suka hadu domin warware matsalar kuma inda ba ta samu jinin ba, Allah kadai ya san abun da ka iya faruwa da matar.

An kiyasta cewa dubban mutane ne ke rasa rayukansu a nahiyar Afirka kowace rana sakamakon rashin jini, saboda haka ministan kiwon lafiya Dr Iliyasu Idi Mainasara ke ganin wajibi ne a dauki matakan gaggawa domin magance matsalar. Ya ce sanadiyar karancin jini mata da yara suna mutuwa kana wadanda suka samu hadarin mota idan ana bukatar jini sai a shiga matsala.

Inji ministan ba'a sayar da jini kuma duk wani likitan da ya sayar da jini ya sabawa doka, za'a hukumtashi.

Bincike ya nuna cewa shakkun da mutane ke da su wajen bayar da jini sune babban dalilan da ke haddasa karancin jinin. Mutane na tsoron kada a bayyana cutar da ke jikinsu idan sun bada jini aka kuma tantanceshi. Sai dai ministan kiwon lafiya ya ce babu wanda zai san ciwon dake cikin jikin wanda ya bada jini. Ba za'a bayyana ba. Ya ce babu wanda zai san wani ya je ya bada jini. Ana tace jini ne da lamba ba da sunan wanda ya bada jinin ba.

Domin kawar da jahilcin jama'a ma'aikatar kiwon lafiya ta shira kemfen din fadakar da jama'a akan bayar da jini a matsayin wata gagarumar hanyar jinkai ta ceto rayuka.

Souley Barma na da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Nazarin Hanyoyin Magance Matsalar Karancin Jini A Asibitocin Nijar - 2' 43"