Matsalar Fasinjojin jiragen sama a Nigeria

Murtala Muhammed International Airport in Lagos, Nigeria (File Photo)

Sau tari dai irin wadannan fasinjoji ana barinsu a tasha ba tare da daukar matakan jin dadinsu ba.

Alhaji Ado Dansudu shugaban wata kungiyar yan Arewcin Nigeria a jihar Legas ya nuna damuwarsa ainun game da yadda kamfanonin jiragen sama ke hulda da fasinjojinsu.

Suma kamfanonin jiragen saman suna irin wadannan kalubala da karancin man fetur da su kan fuskanta kamar yanda Captain Ado Sanusi shugaban kamfanin jiragen saman Aero Contractors yayi bayani. Yace karancin mai shine ke sa kanfanonin jiragen saman masu zaman kansu soke tashin jirage.

A wata hira da wakili sashen Hausa Nasiru El Hikaya yayi da, ministan sufuri Sidika, ya tabbatar da maganar kamfanonin jiragen cewar karancin mai ke haifar da soke tsahin jiragen wanda haka ke kawo cunkuso a tashoshin jirage. Sai dai ya kara da cewar rashin mai ba laifin ma’aikatar sufurin jiragen sama ba ne.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGERIA FILGHTS