Matawalle Ya Yi Wa Dokar Ba Da Fansho Mummunar Fahimta - Ikra Bilbis

Ikra Aliyu Bilbis

Bayan da gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya rattaba hannu akan sabuwar dokar da ta soke tsarin biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu kudaden fansho.

Tsohon ministan sadarwar Najeriya, Alh. Ikira Aliyu Bilbis, ya ce "rashin fahimtar wannan dokar da kantoman rikon jihar Zamfara ya yi, shi ya sa shi soke dokar."

Bilbis na maida martini ne kan soke dokar da aka yi, wacce ta haramta biyan kudaden daga yanzu.

Ikra Aliyu Bilbis

A cewar shi, ita wannan dokar, ba kawai a jihar Zamfara ake da ita ba, kuma ba tsohon gwamna Abdul’aziz Abubakar Yari ya kirkiro ta ba, don haka gwamnan ya yi ma dokar mummunar fahimta.

Ya kara da cewar, ai dalilan da suka sa gwamnan wadannan kalamai da aika-aikar, don bai san yadda aikin yake ba ne, kuma don ba zabar shi aka yi ba, shi ya sa ba shi da masaniyar yadda aikin gwamna yake.

Matsayin shi na Kantoman riko, ya kamata ya din ga mutunta doka, inji tsohon minsitan.

Batun da ya kai ga soke dokar, ta samo asali ne bayan da tsohon gwamnan jihar ta Zamfara, Yari, ya nemi gwamnati mai ci da ta biya shi kudaden fanshonsa na wata-wata, wadanda yawansu ya kai har naira miliyan 10.

A wasu jihohin Najeriya, akan ginawa tsoffin gwamnoni da kakakin majalisu gidaje da biyansu makudan kudaden fansho, don dai a kyautata masu saboda irin aikin da suka yi na bautawa jiha.

Your browser doesn’t support HTML5

Matawalle Ya Yi Wa Dokar Ba Da Fansho Mummunar Fahimta - Ikra Bilbis