Matasan Najeriya Sun Gaji Da Mulkin Tsofaffi

‘Yan kungiyar matasan nan ta ‘NOT TOO YOUNG TO RUN’

Masana harkokin demokaradiyya da shugabanci a Najeriya na ci gaba da fashin baki dangane da yadda ya kamata alaka ta kasance tsakanin dattawa a kasar da suka kwashe shekaru da dama suna rike da madafun iko a matakai daban daban.

Tun ba yanzu banagrorin biyu ke zargin juna, yayin da matasan ke korafin cewa, dattawan sunyi babakere akan madafun mulki, su kuwa dattawan na cewa ne, matasan sun fiye ci da zuci.

Wannan ta sanya har-ma wasu daga cikin ‘yan najeriya ke ganin ya kamata matasan suyi taron dangi domin kwace madafun mulkin daga tsaffin, ganin cewa, zabukan badi na karatowa.

Dr Sa’idu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero Kano yayi fashin baki. Yace masana sun fadi cewa shugaba na koli kada ya gaza shekara 50, amman wadansu basu ambaci shekaru ba sai dai kuma wajibi ne shugaba ya koshi da ilimi da sanin aladar al’umma, ya kamata a tafi da tsarin siyasa da dattijai domin tsawatarwa da matasa da zasu goge su karbi matsayin dattawan a gaba.

Umar Liman Danfulani guda cikin matasan Jam’iyyar PRP a zamanin Jamhuriya ta 2 a Najeriya wanda ke ci gaba da bibiyar lamuran siyasa da shugabanci na cewa. Matasa suna da yarinta don haka mulki bai kamace su ba.

To amma duk da haka, Abubakar S. Umar yace akwai matasa masu kwazo, sai dai dattawan ne ke dakile musu karsashi inda yace akwai wadanda zasu iya yin mulki amman iyayaen gidan su baza su barsu suyi abinda suke so ba

Dokar karfafawa matasa gwiwar tsayawa zabe na cikin dokoki 12 da majalisar dokokin najeriya ta mikawa shugaba Buhari domin ya rattaba musu hannu.