Gabanin taron ‘yan kabilar Ijaw a Abuja Zainab Akasobo Abiola, matar marigayi Chief M.K. O. Abiola wadda kuma ita ce sarauniyar Kalabari, tayi tambaya tana cewa menene ya sa mutanensu suna ganin gwamnatin Buhari ta mayar dasu saniyar ware. Me ya sa suna ganin basa iya kaiwa gareshi?
Manufar taron ‘yan kabilar Ijaw dake Abuja shi ne su nuna basa tare da ‘yan tsageran Niger Delta, yankin da suka fito. Inji Zainab matasan sun tuntubeta domin komawa tsageranci amma ta taka musu birki domin baiwa shugaban kasa Muhammad Buhari damar karfafa muamala da al’ummar yankin.
Zainab ta ce Shugaba Buhari tamkar uba yake ga al’ummar yankin. Injita koina aka shiga walau ofisoshi ko fadar kowane sarki za’a ga hotunan shugaban kasa. Idan bas a sonshi ba za’a go hotunansa koina ba. Tana ganin wadanda suke tare da shugaban ne suke kawo cikas.
Matasan sun ce bas a tare da ‘yan tsageran yankinsu. Sakataren matasan y ace suna da kwarin gwuiwa da tattaunawar da sarakunansu suka yi da gwamnatin Buhari. Suna da kwarin gwuiwa da kowane irin shiri gwamnatin tarayya zata yi domin raya yankinsu.
Babban mai jawabi a taron Manjo Hamza Al-Mustapha y ace ko menene ma suke nema rungumar salama zai fi masu kuma shi zai kaisu ga nasara.
Da yake yiwa Muryar Amurka bayani Manjo Hamza Al-Mustpha y ace a tafiyar da ya keyi dasu a Abuja matasan a shirye suke su fallasa asirin wadanda suke yankinsu da har yanzu suna dauke da makamai.
Bukatun matasan sun hada da kaurar da kamfanonin mai, kammala aikin tsaftace Ogoni da kuma fara aikin gina jami’ar fasahar teku.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5