Matasan Diffa Sun Gaji da Zaman Kashe Wando

Matasa a Jamhuriyar Nijer

Matasan yankin Diffa na Jumhuriyar Nijer sun koka a kan halin zaman kashe wandon da suka tsinci kansu a ciki sakamakon tabarbarewar tsaron da ta biyo bayan rikicin Boko Haram da yankin ya sha fama dashi

Shawarar rufe ma’aikatar hakar zinari ta JADO ta kara tsananta al’amura kana kuma ta haddasa tsayawar harakokin matasa cik a yankin Diffa. Matasan sun yi kira ga ma’aikatar tayi wani abu akan wannan matsalar ta rashin aiki.

Matasan da suka dogara kacokan a kan sana’ar jigilar mutane da babur sun koma aiki a ma’aikatar ta JADO bayan hukumomi sun hana jigilar babur, don haka rufe JADO wani babban kalubale ne da kuma karin matsaloli garesu.

Shugaban matasan yakin Diffa shine ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka Suleiman Mumuni Barma halin da matasan ke ciki a cikin wata hira da yayi dashi, inda ya kara da cewa harkar Boko Haram itace ta haddasa duk wadannan matsaloli da suke fuskanta a yanzu.

Your browser doesn’t support HTML5

Diffa