Matasan da Gwamnatin Gombe ta Dauka ta Horas Sun yi Bori

Matasa

Makon da ya gabata gwamnatin jihar Gombe ta dauki matasa dubu biyu domin ta horas da su kan ayyukan da suka jibanci sa kayan sarki
Jiya matasa 2000 da gwamnatin jihar Gombe ta dauka da suke samun horo game da ayyukan da suka jibanci sanya kayan sarki suka gudanar da bori domin nuna rashin dadinsu da irin salon koyar da su.

Rahotanni na nuni da cewa kusan kashi sittin cikin dari na matasan sun bar sansanin. Daya daga cikin wadanda suka bar wurin horon yace mutane ana gana masu wahala, ana gana masu gwale-gwale. Yace horaswar kamar ta soja take. Yace su sun gaji domin azabar ta yi yawa. Yace horaswar ta wuce misali. Yace abinci ba za'a bari ka ci ba. Kana cin abinci ana razanaka, kana ka sheka da gudu. Yace ko salla ma ba za'a barka ka yi ba.Yace wahalar ta yi yawa su kuma ba aikin soja aka daukesu ba.

Dangane da ko dama basu da masaniyar abun da za'a horas da su sai yace an ce masu akwai aikin sufuri wato yadda ake ba motoci hanya da tsaron unguwanni. Ayyukan suna nan kala-kala amma su basu san abun ba.

To saidai kwamishanan kananan hukumomi da masarautu na jihar Alhaji Abubakar Ahmed Walama ya ziyarci sansanin da ake horas da matasan dake garin Malam Sidi. Yace matsalar yara ce kawai da basu saba da irin horon ba amma zasu cigaba kodayake 'yansandan jihar sun ce basu da labari kan lamarin amma sun tura jami'ansu.

Ga cikakken rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan da Gwamnatin Gombe ta Dauka ta Horas da Su Sun yi Bori - 2:59