An gudanar da wani taro akan matasa a Jami’ar Bayero ta Kano, inda rukunin matasan arewa maza da mata sukayi musayar ra’ayoyi akan al’amura guda tara masu alaka da makomar rayuwarsu a matakai daban daban.
Farfesa Aisha Abdul, Daraktan cibiyar nazarin jinsin bil-Adam, da bincike kan harkokin ci gaban al’uma ta Jami’ar Bayero dake Kano, ta ce makasudin wannan taro shine domin sanin damuwar matasa shi yasa taken taron ya kasance “Matasan Arewa Mai Kuke So”.
Ta kara da cewa an ware fannoni guda tara da suka hada da harkokin samarda aiki, Ilimi, cin hanci da rashawa da kuma sha’anin tsaro da gyara tunanin matasa, da halayya da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Taron na hadin guiwa ne tsakanin cibiyar nazarin jinsin bil-Adam, da takwararta ta Cibiyar Kukah, wanda Rev. Hassan Mathew Kukah, ya assasa.
Masana a fannonin daban daban sun gabatar da Makala, Dr. Bala Muhammad,daya daga cikin wadanda su kayi jawabi yace, ya kamata Gwamnati ta fara tunani cewa duk abinda zata yi na zana abinda yakamata ayi ga matasa toh a tabbatar da cewa matasan na ciki kuma ba matasa ‘yan boko kadai ba har wadanda ba suyi boko ba domin suma suna da kwakwalwa, sun san abinda suke so kuma sun san abinda yakamata ayi.
Daga bisani an baiwa matasa dama dasu su wasa kwakwalwa akan matakai da hanyoyin warware kalubalen dake barazana ga makomar rayuwarsu.
A Saurara domin karin bayani........
Your browser doesn’t support HTML5