Nura Ahmad Yadi Bichi – Dokar da aka sanyawa hannu ta baiwa matasa damar a dama da su a harka ta siyasa, 'Not too young to run' ta zama kalubale ga matasa duba da yadda ake tauye masu hakki a harkokin cigaban kasa.
Yana ganin abunda ya haddasa rashin baiwa matasa dama bai wuce rashin bada muhimmanci a fannin siyasa da cigaban kasa, ya samo asali ne da rashin jajircewa da maida hankali inda mafi yawan matasa ke shiga dabi’un batanci da rashin madafa.
Comrade Nura, ya kara da cewa kwadayi da son abin duniya ya jefa matasa ga matsalar da suke ciki a yanzu, da rashin maida hankali wajen yin karatu da sanin ainihin abinda kasa ta ke ciki, ta hanyar baiwa matasa damar nuna nasu bajinta.
Comrade, ya kara da jan hankalin matasa da suyi hakuri da kwadayi da mai da hankali wajen ceto matasa daga cikin kangin da suke ciki, inda ya ce a yanzu suna hada taruka da zasu wayar da kan matasa wajen yin gwagwarmayar kwato wa kansu yanci.
Ya ce matasa ne da kansu zasu karbo damar da suke da ita, ta samun gurbi a fannin siyasa domin kawo sauyi ga yadda siyasar Nijeriya ke wakana, sannan yana da yakinin a zabe mai zuwa, a karon farko matasa zasu kai ga gaci, tare da bada misalin matasan shugabannin da suka mulki Nijeriya a wancan lokaci suka kuma yi wa kasa hidima.
Your browser doesn’t support HTML5