Matasa Sun Koka Da Rashin Tafiya Da Su A Gwamnatin Buhari

  • Ibrahim Garba

Taron wasu matasa

Yayin da gwamnatin Najeriya ke cigaba da nade-naden jami'anta, matasa na kokawa kan rashin sasu cikin gwamnati

Kakakin Majalisar Matasan Najeriya Honorabul Abba Waziri y ace matasa ba su ji dadin rashin damawa da su a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba. Ya ce bai kamata gwamnati ta fara da kin tafiya da matasa ba, ganin rawar da matasa ke takawa da kuma wadda su ka taka a zabukan da su ka gabata cikin nasara.

Da yak e magana da wakilinmu a Abuja Hassan Maina Kaina, Kakakin na matasa y ace akwai matasan da su ka goge a fannoni daban-daban ta yadda kowane irin matsayi ka bai wa matasan Najeriya ba za su kasa ba.

Ita ma wata ‘yar rajin kare hakkokin matasa a Najeriya mai suna Fatima Maina Abdullahi ta ce matasa sun dauka cewa Buhari zai bai wa matasa kaso a gwamnatinsa sai gashi an barsu a tutar babu. Don haka Fatima ta ce yakamata a yi kwaskwarima ma sunayen da aka gabatar don a bai wa matasa wasu mukamai.

To amma Honorabul Mai Mala Boni, Sakataren jam’iyyar APC mai mulkikn Najeriya y ace akwai matasa isassu a gwamnatin Buhari ciki har da Ministocin da aka gabatar daga jahohin Kebbi, Borno, Yobe Kaduna da sauran mukamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Sun Koka Da Rashin Tafiya Da Su A Gwamnatin Buhari -2'39''