A jiya Laraba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da majalisar ministocin sa su arba’in da uku a birnin tarayya Abuja.
A wata hira ta musamman da Muryar Amurka, sabon ministan matasa da wasannin Najeriya, tsohon shugaban sashen Hausa na Muryar Amurka kuma, Sunday Akin Dare, ya ce akwai abubuwa da yawa dake damun matasan Najeriya da suka hada da rashin aikin yi da kuma rashin damar samun ilimi. A saboda haka, ma’aikatarsa zata fito da wasu shirye shirye da zasu taimakawa matasan.
Mr. Dare ya kuma ce abu na farko da zai fara maida hankali aka shine samarwa matasa ayyukan yi, musamman wadanda suka kammala karatun su amma babu ayyukan yi, da kuma wadanda basu sami damar zuwa makaranta ba amma su na sha’awar wasanni, ma’aikatar zata nemo su, ta ba su ilimi.
Yanzu dai abin da ‘yan Najeriya musamman matasa suka zuba ido su gani shine yadda rayuwarsu za ta inganta a wannan wa’adin na biyu na mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Your browser doesn’t support HTML5