Matasan Najeriya musamman na Borno sun bukaci tsofofin 'yan siyasa su basu dama su karbi ragamar jan shugabancin kasar Najeriya.
WASHINGTON, DC —
A dai dai lokacin da aka soma samun kwanciyar hankali daga hare-haren kungiyar Boko Haram wadda ke da tushenta a jihar wani abun da ya soma daukar hankalin jama'a kuma shi ne batun siyasa.
Yadda 'yan siyasa ke canza sheka daga wannan jam'iyya zuwa waccan ya zama kamar caca haka kuma batun PDP da sabuwar jam'iyyar PDP. Ana wannan kuma sai wasu matasa suka soma ikirarin lokaci ya yi da za'a bar masu damar jan ragamar shugabancin jihar da ma kasar domin a samu cigaba.
Waddan nan harkokin siyasa sun haifar da cecekuce da nune nunen yatsa ma juna a jihar . A bangaren matasa sun ce sun gaji da yadda ake gudanar da mulkin kasar. Sun koka da yadda aka hana su taka rawar gani a harkokin mulki sai dai a yi anfani da su wurin neman zabe. Da zara an gama zabe kuma sai a yi watsi da su. A cewarsu wannan lokacin ya wuce. Malam Muhammed Shettima Kuburi daya daga cikin shugabannin 'yan siyasa matasa a Najeriya ya ce kada ayi anfani dasu a matsayin sojojin siyasa. Ya ce akasarin gaskiya ma matasa su ne manyan gobe. A kasashe da suka cigaba matasa 'yan shekaru 30 ko 40 na rike mukaman shugabancin majalisu har ma na dattawa amma a Najeriya da an tabo wannan batun sai a ce dan shekara 30 ko 40 yaro ne. Hankali da sanin ya kamata su ne suke duba babba amma ba shekara ba.Domin haka acewarsa lokaci ya yi da za'a basu dama su tsaya takarar kowace kujera a Najeriya.
Wadanda suka hade cikin sabuwar jam'iyyar APC sun ce sun yi hakan ne domin kawar da rashin zaman lafiya da yunwa da talauci da rashin aikin yi a kasar. A ganinsu 'yan Najeriya sun gaji da irin mulkin da ake yi masu. Najeriya na bukatar canjin shugabanci da akida.
Ga cikakken rahoto.
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”

Your browser doesn’t support HTML5