MATASA A DUNIYAR GIZO: Yadda Za A Yi Amfani Da Kafafen Sada Zumunta Wajen Samar Da Zaman Lafiya - 26 Satumba, 2021

Shamsiyya Hamza Ibrahim

Shirin "Matasa A Duniyar Gizo" na wannan mako, ya karbi bakuncin kungiyar Young Man Afirka wacce ta gudanar da taron bita kan yadda za a mayar da hankali kan rawar da al’umma za ta taka wajen yada zaman lafiya ta kafafen yada labarai na yanar gizo.