Matakin "Operation Sharar Daji" Ya Bude Zirga Zirga Tsakanin Zamfara Da Katsina

Sojojin saman Nigeria dake yaki da muggan mutane a Zamfara

Irin nasarorin da sojojin Nigeria ke samu a fafatawar da su keyi da 'yan bindigan dazukan Zamfara a sama da kasa ya sa lamuran zirga zirgan ababen hawa soma daidaitawa tsakanin Zamfara da Katsina

Kakakin runduna ta daya na sojojin Nigeria Kanar Muhammad Dole ya ce tunda suka soma fafatawa da miyagun mutanen da suka addabi jihar Zamfara an samu nasarori sosai saboda satar shanu, kashe mutane da sace mutane domin neman kudin fansa sun ragu ainun.

Shi ma kakakin hedkwatar rundunar sojojin saman Nigeria Air Commander Ibikunle Daramola, ya tabbara da kalamun Kanar Dole tare da cewa, ko a jiya ma sojoji sun karkashe 'yan bindiga da dama a Bayan Ruwa, da Dajin Rugu dake gabashin jihar Zamfara.

Birgediya Janar Maharzu Tsiga shi yake sa ido a fafatawar da sojojin ke yi da 'yan bindigan dake samun mafaka a cikin dazukan Zamfara. Ya tabbatar da babbar nasarar da sojojin ke samu walau a kasa ko a sama.

Biyo bayan nasarorin da sojojin ke samu zirga zirgan ababen hawa tsakanin Zamfara da Katsina ya fara komawa daidai. Shugaban kungiyar direbobin Katsina Alhaji Jamilu Sha'aibu ya ce yanzu sai su yiwa Allah godiya saboda direbobinsu suna lodi daga Katsina zuwa Zamfara, haka kuma daga Zamfara zuwa Katsina ba tare da samun wata matsala ba a kan hanya.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarorin Sojoji A Zamfara Ya Sa Lamuran Sufuri Zuwa Katsina Su Soma Daidaitawa - 2' 26"