Matakin da hukumar tsaron Najeriya ta dauka na sa ido ga yadda ake anfani da kafofin sadarwa musamman Facebook, ya samu rashin karbuwa ga masu rajin kare hakin bil Adama.
'Yan ragin kare hakin bil Adama na ganin wani takunkumi ne na hana mutane fadin albarkacin bakinsu kamar yada Barrister Atiku Ismaila ya bayyana.
Yana mai cewa aikin sojoji ne su kare kasa da tabbatar cewa ta cigaba da zama kasa daya. Ya ce akwai hukumar tsaron cikin gida ita ke da hakin daukan mataki. Yana cewa a bar masu aikinsu. Kada wani ya shigo ciki. A cewarsa kundun tsarin mulkin kasa ya ba kowa 'yancin fadin albarkacin bakinsa kan ka'ida
Kwamred Garba matakin da sojoji suka dauka ya dace. Yana mai cewa mutane suna da 'yancin fadan albarkacin bakinsu amma suna wuce gona da iri. Matakin zai taimaka wajen kiyaye mutuncin mutane musamman shugabannin kasa. Idan sojojin zasu yi aikin cikin gaskiya wata hanya ce ta kare mutuncin mutane, inji Kwamred Garba.
Sanata Ali Wakili daga mazabar Bauchi ta Kudu yace batun ba na 'yan siyasa ba ne. Akwai dokoki kan batun saidai ba'a anfani dasu ne.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5