Matakan Dauka Domin Kare Afkwuwar Haka Nan Gaba

Za a kara sa ido da kuma kara tantance gidajen kallon kwallo a jihar Cross River

Tun bayan hadarin da aka samu na faduwar turken wutar lantarki kan wasu masu kallon kwallon kafa a jihar Cross River a baya bayan nan jama’ar jihar dama ma na kasa baki daya na ci gaba da nuna alhinin hakan kuma tun lokacin ne ake ta bin diddigin abindfa ya faru da kuma irin matakan da ake dauka domin kaushewa sake afukuwar hakan nan gaba.

Wani masanin harkar lantarki Inginiya Habib Abdullahi, yace wayar wuta mai jawo wuta daga babban layin wutan lantarki wayar ce mai nagarta mawuyacin abune ace an sami irin wannan ya faru idan dai wannan wayar da aka yi amfani da ita ta kasance ingantatciya.

Tuni dai bayanai suka nuna cewa gwamnatin jihar ta Cross River inda lamari ya faru ta bayana cewa zata dauki nauyin biyan kudaden asibiti wadanda suka samu raunuka a sanadiyar wannan hadari a asibitoci daban daban daga farko kulawa har zuwa samun sauki.

Sai dai kuma alkalluma a hukumance sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai koda yake bayanai masu karo da juna sun bayana cewa addadin yafi haka.

Mai baiwa gwamnan jihar ta Cross River, shawara akan harkokin baki Barrister Musa Maigoro, yace gwamnan jihar, ya bada umarnin kafa kwamitin da zai binciki abinda ya faru domin daukar matakan kare afkwuwar haka nan gaba da kuma kara sa ido aka gine gine a jihar domin tantance su.

Akwai da tarin ‘yan Najeriya, dake da sha’awar kallon kwallon kafa kuma sun yi tsokaci daban daban akan matakan da ya kamata gwamnati ta dauka akan irin wadannan gidajen kallo.

Your browser doesn’t support HTML5

Matakan Dauka Domin Kare Afkwuwar Haka Nan Gaba - 3'29"