Matakan Tsaro: Kotu Ta Ba 'Yan Sanda Gaskiya Kan Gayyatar Mailafiya

A cigaba da rigimar da ta biyo bayan wasu kalaman da tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya ya yi game da matsalar tsaro a Kudancin Kaduna, wata kotu a Jos ta tabbatar da hurumin hukumar 'yan sandan da ta gayyace shi

Babban kotun dake jihar Filato a Jos, ta yi watsi da karar da tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya ya shigar, inda yake kalubalantar cancantar hukumar ‘yan sanda kan gayyatar da ta yi masa don binciken wasu kalaman da ya furta yayin wata hira da wani gidan rediyo a jihar Legas kan rashin tsaro a kudancin Kaduna.

Mai Shari’a Arum Ashoms, ya dauki tsawon lokaci yana karanta bayanai kan hukuncin, ya ce, hukumar ‘yan sanda na da hurumin gayyatar kowa don samun bayanai.

Obadiah Mailafia 2

Jagoran lauyoyin dake kare Dr. Obadiah Mailafiya, Barista Yakubu Sale Bawa, ya ce za su yi nazarin hukuncin kafin daukar mataki na gaba.

Lauyan bangaren hukumar ‘yan sandan Najeriya, Barista Michael Mayowa Oladipo, ya ce kotu ta yi adalci, soboda hukumar ‘yan sanda na da ikon neman bayyanai a wurin al’umma, kuma hakkin ‘yan kasa ne su bayar da bayyanai ga ‘yan sanda musamman kan abinda ya shafi harkar tsaro.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Mailafiya