Mataimakiyar Shugaban Amurka Ta Fara Ziyarar Aiki A Ghana

Kamala Harris Ta Sauka A Ghana Don Fara Ziyara Aiki Mai Cike Da Tarihi Zuwa Wasu Kasashen Afirka

Mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris ta samu tarba daga 'yan makaranta da masu kade-kade da raye-raye na gargajiya, a lokacin da ta isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kotoka na kasar Ghana.

Mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris yayin da take jawabi jim kadan bayan saukarta a filin tashi da saukar jiragen sama na Kotoka, da ke Accra, ta ce shugaban kasa da daukacin al'ummar Amurka na mika gaisuwa tare da fatan wannan tafiya za ta kara kyakkyawar alaka da abota tsakanin al'ummar Amurka da mazauna nahiyar Afirka.

Ta bayyana kudurinta na gudanar da tattaunawa da za ta samar da damarmaki a sassa daban-daban na nahiyar da za su amfani al’ummar nahiyar da ma duniya baki daya.

A cewar Kamala, ganawa da za ta yi da Shugaban Ghana da shugabannin Tanzaniya da Zambiya, za su dora daga inda suka tsaya a tattaunawa da su ka fara a taron Afirka da aka gudanar a Amurka watannin baya, kan karfafa dimokradiyya da shugabanci na gari, da samar da zaman lafiya da tsaro, da bunkasar tattalin arziki mai dorewa, da karfafa huldar kasuwanci.

Kamala Harris Ta Sauka A Ghana Don Fara Ziyara Aiki Mai Cike Da Tarihi Zuwa Wasu Kasashen Afirka

Mataimakin shugaban kasar Ghana, Dakta Mahamudu Bawumia ne ya jagoranci jami’un gwamnati da suka tarbe ta, kewaye da masu kide-kide da raye-rayen gargajiya da ‘yan makaranta suna daga tutocin Ghana da na Amurka.

Mai sharhi kan hulda tsakanin kasa da kasa da kuma tsaro, Irbard Ibrahim ya ce baya ga alaka mai kyau ta diflomasiya da ta kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu, haka kuma ziyarar ba za ta rasa alaka da zawarci da kasashen Rasha da China ke yi ga nahiyar Afirka ba.

Ya ce, Ghana na marhabin da zuwanta kuma kofofin diflomasiya ta Ghana na bude ga ziyarar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris.

A yayin ziyarar mataimakiyar shugabar kasa Kamala Harris, za ta gana da shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo a ranar Litinin domin tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Yunus Swalahudden Wakpenjo, ya ce, fatar ita ce a kara dankon zumunci ta fannin siyasa, diflomasiya da tattalin arziki. Haka kuma yake burin duk tattaunawar ta zama akwai dangantaka da yanayin tsadar rayuwa da Ghana ke fama da shi a yau.

Uwargida Kamala Harris za ta ziyarci gidan wasan kwaikwayo kuma ta sadu da matasa dake masana'antar kere kere, bayan ganawarta da shugaban Akuffo-Addo.

A ranar Talata za ta gabatar da jawabi ga matasa, kuma za ta ziyarci gidan adana bayi mai tarihi dake birnin Cape Coast, inda za ta yi jawabi kan illar da safarar bayi ta yi ga nahiyar Afirka.

Domin karin bayani ga rahotan Idris Abdullah Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakiyar Shugaban Amurka Ta Fara Ziyara Aiki A Kasar Ghana - 3'14"