Mutumin da ya zama Mataimakin Shugaban Sudan Ta Kudu na farko, Riek Machar, da matarsa Ministar Tsaro Angelina Teny, sun kamu da cutar COVID-19, wadda kwayar cutar corona ke haddasawa.
“Ina son in bayyana cewa, ni, Mataimakin Ciyaman din babban kwamitin Aiki Da Cikawa, na kamu da cutar COVID-19. Akwai kuma wasu mutanenmu da su suka kamu da cutar. Abin da zan iya fada a yanzu kawai shi ne, Madam Angelina Teny, Ministar Tsaro, ita ma ta kamu,“ a cewar Machar a wani jawabin da aka yada ta gidan talabijin na kasa baki daya.
Sakataren Yada Labaran Machar, James Gadet, ya tura wani sako ta shafinsa na Facebook, yana mai tabbatar da cewa mai gidan nasa ya kamu da cutar corona.
“Maitaimakin Jamhuriyar Sudan Ta Kudu, Mai Girma Riek Machar Teny-Dhurgon da Madam Angelina, da wasu hadimansa da dogarawansa, sun kamu da cutar COVID-19.” A cewar Gadet.
Kafin makon jiya dai Teny ya kasance Mataimakin Ciyaman din Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 a kasar.