Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Matasan Arewa Maso Gabashin Nigeria

Farfesa Yemi Osinbajo mataimakin shugaban Najeriya da Injiniya Babale mataimakin gwamnan Adamawa

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arzikin matasan jihohin arewa maso gabashin Nigeria, a Yola babban Birnin jihar Adamawa

Da yake jawabi wajen kaddamar da wannan sabon shiri na tada komadar tattalin arzikin matasan arewa maso gabashin Najeriya, jihohin da bala’in Boko Haram ta fi shafa a Najeriya, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, ya bayyana kudurin gwamnatin Najeriya na samar da yanayi,da kuma sinadaran da suka wajaba,na tada tattalin arzikin al’umman wannan yankin dama Najeriya gaba daya.

Yemi Osibanjo,wanda mataimakin gwamnan jihar Adamawa Injiniya Martins Babale ya tarba,yace muddin ana son Najeriya ta ci gaba sai gwamnatoci sun maida hankali wajen fannin kimiya da fasaha da kuma kere-kere,kamar yadda lamarin yake a kasashen da suka ci gaba.

Yace matasan Najeriya na bukatar ta shi tsaye ta fannin kere kere da samar da hanyoyin dogaro da kai,don haka ne aka zakulo wadanda suka kware guda 25 daga fannoni da dama da za’a horas a kuma tallafawa domin suma su taimaka a yunkurin gwamnati na sake gina wannan shiya da rikicin Boko Haram ta daidaita.

‘’Nan gaba,baya ga na wannan shiya,za’a kuma kaddamar da wannan shiri a sauran bangarorin Najeriya shida, da daya a jihar Lagos da kuma babban birnin tarayya, Abuja.’’

Suma a jawabansu mukaddashin gwamnan jihar Injiniya Martins Babale da kuma sakataren gwamnatin jihar Adamawa Dr Umar Bindir dukkaninsu sun yaba da wannan shiri.

Mallam Fahad Garba Aliyu, daya daga cikin wadanda aka gayyata domin bada shawarar,ya bayyana irin gudummawar da zasu bada. Y ace su shida aka gayyato su ga abubuwan da suke dashi kana su bada shawara tare da koyas dasu abun da ya kamata su sani.

Shi dai wannan sabon shiri baya ga gwamnatin Najeriya,akwai sa hannun kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross,ICRC a takaice, dake da zummar maida hankali kan yan gudun hijira.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Matasan Arewa Maso Gabas – 2’ 19”