Gwamnatin kasar Cuba tace mataimakin shugaban kasa na farko Miguel Diaz-Canel Bermudez, shi kadai ne dan takara na shugaban kasa da aka gabatar dashi, matakin da ya tabbatar zai zama shugaban kasar ta kwaminisanci na farko da bashi da nasaba da iyalan Castro da suka kwashe kusan shekaru sittin suna mulkin kasar.
Gabatar da mataimakin shugaban kasar zata bukaci amincewar majalisar kasar, wacce take da tarihin amincewa da wadanda aka gabatar mata dasu.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert tace sauya mulkin kasar, al’amari ne da gwamnatin Trump take nuna damuwa akai, saboda ba’a gudanar bisa tsarin mulkin demokaradiya ba