Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence zai kai ziyara Munich da Brussels a cikin ‘yan kwanki masu zuwa, ziyararsa ta farko kasar zuwa waje tun da aka rantsar da shi a watan da ya shige.
WASHINGTON D.C. —
Wani babban mashawarcin fadar White House kan harkokin kasashen ketare ya ce, ziyarar, dama ce ga mataimakin shugaban kasar ta kara ba abokan kawancen Amurka tabbaci da kuma bayyana tsare-tsaren Amurka a madadin shugaba Donald Trump.
Shugabannin kasashen turai suna bayyana fargaba a kan shugabancin Trump bayan da shugaban kasar ya yi ta yaba shugabancin Vladimir Putin, da kuma yadda Trump ya bayyana kungiyar tsaro ta NATO a matsayin tsohuwar yayi.
Pence zai yi jawabi a wajen taron harkokin tsaro da za a gudanar a Munich, da mashawarcin na Fadar ta White House ya ce Pence zai ba abokan kawancen Amurkan tabbacin goyon bayan kasar.