A wani lokaci yau Talata ake sa ran mataimakin shugaban Amurka Joe Biden zai gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin kasar Ukraine, kwana daya bayan da ya bada sanarwar sabon tallafi da Amurka ta baiwa kasar na dala miliyan 190.
Mr. Biden ya fada jiya Litinin cewa, sabon tallafin zai taimakawa kasar ta aiwatar da sauye sauye kuma ta yaki cin hanci da rashawa.A lokacinda suke ganawa da manema labarai ta hadin guiwa bayan shawarwari da ya gudanar da shugaban kasar Petro Poreshenko,Biden yace, "wajibi ne ga Ukraine, domin ta kasance ta sami daidaito, da bunkasa a turai, ta tabbatar da cewa babu wata kunbiya-kumbiya ta kawar da cin hanci da rashawa baki dayansa, matsalar da ya kwatanta da cutar kansa.