Kungiyar yayata manufofin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wadda da turancin Ingilishi ake kira Jonathan Actualization Movement - JAM a takaice - ta je Sokoto ta yi babban taron zaman lafiya na yankin arewa maso yammacin Najeriya.
A cikin jawabin da ta yi a wajen taron gangamin, shugabar kungiyar ta tallata manufofin shugaba Goodluck Jonathan, Otunba Basirat Nahibi ta ce a daina ganin laifin shugaban game da matsalolin tsaron da ake fama da su a yankin arewacin Najeriya.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a shiyyar, Murtala Faruk Sanyinna ya halarci taron gangamin kuma ga rahoton da ya aiko:
Your browser doesn’t support HTML5
A yayin da magoya bayan shugaba Goodluck Jonathan ke karfafa mi shi guiwar cewa ya tsaya takarar neman zarcewa da mulki a shekarar dubu biyu da goma sha biyar, masu sukan lamirin shi cewa suke yi, ya yiwa kan shi adalci, kuma ya yiwa Najeriya adalci kar ya tsaya takara saboda gwamnatin shi ta gaza ta kowane fanni.
Wani abun lura kuma, shi ne cewa irin wadannan tarurrukan gangami masu kama da yakin neman zabe da magoya bayan shugaba Goodluck Jonathan ke ta yi, na faruwa ne a shiyoyin kasar ta Najeriya daban-daban a daidai lokacin da Sufeto janar na 'yan Sanda Suleiman Abba ya kafa wani sashen kula da al'amuran zabe musamman ma saka ido kan masu yin yakin neman zabe kafin lokaci.