Mata 'Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar Sun Bayyana Matsalolinsu

Yayinda ake bikin tunawa da ranar ‘yan jarida ta duniya a yau 3 ga watan Mayu ‘yan jarida mata a jamhuriyar Nijer sun koka game da wasu matsaloli dake katse masu hanzarin aiki, lamarin dake tayar da hankulan kungiyoyin ‘yan jarida mata.

Aikin jarida na daga cikin ayyuka na gaba-gaba da mata suka runguma a jamhuriyar Nijar tun daga lokacin da kasar ta tsunduma a tafarkin dimokradiyya kawo yau, sai dai bayanai na nunin ‘yan jarida mata ba sa samun sukunin gudanar da aikin kamar yadda ake bukata sanadiyar wasu matsaloli.

Malama Salamatou Mai Daji ‘yar jarida ce mai zaman kanta, ta ce ba a ba mata dama kamar yadda ya dace musamman a fannin rike mukamai a kasar.

Karancin albashi da rashin sakin ragamar gudanar da aiki su ma wasu matsaloli ne na daban dake yiwa ‘yan jarida mata tarnaki inji Harieta Sala, ita ma wata ‘yar jarida mai zaman kanta.

Yanzu haka Kungiyar APAC ta matan Afirka ma’aikatan watsa labarai reshen jamhuriyar Nijar ta fara yunkurin samar da hanyoyin warware wadannan matsalolin kamar yadda shugabar kungiyar Amy Niandou ta shaida. Ta ce kungiyar ta kafa wasu hanyoyi da zasu taimaka nan gaba, musamman ta fannin bada mukamai ga mata masu hazaka a aikin su.

Dokokin Nijar sun yi tanadin kaso na musamman domin mata a duk lokacin da ake rabon mukaman shugabanci saboda haka shugaban hukumar sadarwa ta CSC Dr. Kabirou Sani ke yin kira ga shuwagabanin kafafen yada labarai akan wannan magana.

Nauyin da ya wajaba a wuyan kafafen yada labarai domin ci gaban dimokradiyya na matsayin wani maudu’i da tawagaogin kasashen Afirka ke tattaunawa akai a garin Addis Ababa albarkacin ranar 3 ga watan Mayu, wato ranar ‘yancin aikin jarida.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata 'Yan Jarida A Jamhuriyar Nijer Sun Bayyana Matsalolinsu - 2'59"