Mata Sun Hana Motoci Wucewa.

  • Ladan Ayawa

Taron mata masu yoyon fitsarin da aka yi wa tiyata a jos

A hirar wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Andulwahab Mohammed da mai magana da yawur ‘yan sandan jihar Gombe DSP Obed Mary Maglum ta tabbatar da aukuwar lamarin da kuma iri matakan da aka dauka domin kawar da matar kan hanya.

Tace da gaske ne mata sun tsare hanyar Kaltungo,akwai tsare wasu mutane da akayi game da kashe wani Dan Sanda da akayi kwanakin baya wani saje, shi yasa suka fito suka tsare hanya, sunyi haka ne sabo da wannan kamen,’’

Tace suna neman a saki wasu daga cikin wadanda aka kame game da kamun da aka yi.

Taci gaba da bayanin cewa yanzu haka da muke Magana da kai da kwamishinan ‘yan sanda da wakilan sa da kuma shi mai girma Sarkin Kaltungo da kuma dan majilisar dake wakilta wannan yankin da kuma shugaban karamar hukuma, yanzu haka suna nan suna Magana yadda za a yi a bude hanya zasu gana da matar’’.

Ga Abdulwahab Mohammed da Karin bayani 3'03

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Sun Hana Motoci Wucewa