Mata Ne Suka Fi Fuskantar Tarin Matsaloli – Rahoton UNFPA

A wani sabon rahoto da Asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ya fitar, ya yi nazari akan halin da al’ummar duniya ke ciki inda ya gano cewa mata ne suka fi fuskantar tarin matsaloli, rahoton da aka yi wa take da "Ba da son rai na ba,’’ lamarin da ke nuna rashin daidaito tsakanin mata da maza na kara ta’azzara ayyukan cin zarafi akan matan.

Irin wannan rahoto dai a duk shekara ake fidda shi don duba halin da al’ummar duniya ke ciki, inda a bana rahoton ya fi karkata akan halin da mata suka tsinci kansu ciki musamman a wannan lokaci da dokar kulle sakamakon annobar cutar COVID-19 ke dada kara ayyukan cin zarafi ga mata kamar yadda Kori Habib, wacce ke aiki da asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya a fannin hulda da 'yan jarida a Najeriya ta bayyana.

Zanga Zangar Kungiyoyin Mata Kan Fyade

Ta ce akan tozarta 'yaya mata ta hanyar hana su zuwa makaranta, da auren dole, da auren wuri, ko hana mace gado, fyade da sauransu, wadannan abubuwan su suka fi ci wa Majalisar Dinkin Duniya tuwo a kwarya, a cewarta.

Jami’ar lafiya a asibitin tarayya da ke Unguru a Jihar Yobe, Hajja Muhammad, ta bayyana irin illolin da ke tatttare da yi wa mata kaciya wanda hakan wani nau’i ne na cin zarafin su.

Kwamishiniyar harkokin mata a jihar Nasarawa Hajiya Halima Jabiru, ta ce wannan yanayi da duniya ta tsinci kanta a ciki ya farkar da gwamnati musamman a sha’anin da ya shafi kiwon lafiyar mata.

Wani babban kalubale da mata ke fuskanta a Najeriya shi ne batun tabarbarewar sha’anin tsaro da ke hargitsa musu rayuwar iyalinsu a cewar 'yar fafutukar kare hakkin mata Amina Yahaya.

Rahoton na Asusun kula da yawan jama’a a Majalisar Dinkin Duniya na fatan za a kawo karshen jinkirin da ake samu wajen aiwatar da dokar hana yi wa yara mata auren wuri da yi musu kaciya da kuma yawan cin zarafi ta hanyar lalata ko yi musu fyade da aka yi ta samu a wannan shekarar ta 2020.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Ne Suka Fi Fuskantar Tarin Matsaloli – Rahoton UNFPA