Matasa a sasan duniya da dama kan yi korafi kan irin wahalhalunda suke fuskanta wajen neman ayyukan yi idan sun kammala karatunsu.
Aisha Sani Aliyu, matashiya da ta karanci harshen Turanci da addini a Kano, ta ce ta yi karatu ne domin ta taimakawa al'ummarta mussaman ma mata tare da huce wa kai takaicin bani-bani.
Ta ce, duk da cewa ta yi karatu, tana sana’ar dogaro da kai kafin lokacin da za ta samu aikin gwamnati ko wani aiki na zuwa ofis.
Malama Aisha ta ce takan samu odar yin kayan tande-tande daga wajen abokai da kawayen arziki, mussaman a lokutan biki ko wani sha’ani.
Aisha ta ce, a yanzu abin da ke ci wa mata tuwo a kwarya bai wuce yadda mata ke fuskantar matsalar samun aiki bayan sun kammala karatu.
Daga karshe ta ce tana shawartar mata da su nemi ilimi, domin neman ilimi, ba’a girma da shi, tana mai cewa komai girman mace za ta iya fita ta yi karatu domin ta fadakar da al'ummarta.
Your browser doesn’t support HTML5