Mata Masu Sana'a A Kasar Hausa Na Fuskantar Barazana Inji - Rashida Tsakuwa

Rashida Tsakuwa

Babban kalubale da nake fuskanta shine hassada daga wajen makiya inda suke ikrarin cewar ba kasar Saudia nake zuwa don saro kaya ba illa jihar Lagos ko Kwatano inji malama Rashida Tsakuwa.

Ta bayyana haka ne a zantawarta da wakiliyar DandalinVOA , inda ta ce ta yi sana’oi da dama da suka danganci dinki, saka ,kayan koli da sauransu

Ta kara da cewa Sana’a babbar rufin asiri ce ga mata mussamam ma idan mace magidanciya ce , duk kuwa da Karin farashin da aka yi ga kayayyaki ga masu safara zuwa kasar Saudi Arabia hakan bai sa ta daina safara ba.

Rashida ta ce duk macen da ta jajirce wajen neman na kanta a kasar Hausa na fuskantar barazana mussamam ma idan tana safara zuwa kasashen waje, babu irin abinda ba za’a ce tana yi ba. Daga karshe ta ja hankalin mata da su jajirce wajen neman nasu na kansu.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Masu Sana'a A Kasar Hausa Na Fuskantar Barazana Inji - Rashida Tsakuwa