Mata Masu Ciki Dake Da Hawan Jini Suna Da Hadarin Kamuwa Da Cutar Shanyewar Sashin Jiki

Mata masu ciki

Hawan jini yayin juna biyu zai iya kara yawan hadarin da mata ke da shi na shanyewar sashin jiki nan gaba, bias ga rahoton wani binciken da aka gabatas a taron ciwon shanyewar jiki ta Kanada.
Hawan jini yayin juna biyu zai iya kara yawan hadarin da mata ke da shi na shanyewar sashin jiki nan gaba, bisa ga rahoton wani binciken da aka gabatas a taron ciwon shanyewar jiki ta Kanada.

“Mun gano cewa matan da suka sami hawan jinni lokacin da suke dauke da ciki suna da hadarin kamuwa da ciwon shanyewar sashin jiki, musamman idan sun sami wata matsala da ake kira “pre–eklamsiya” wani irin hawan jinni mafi tsanani” inji Dr. Aravind Ganesh, wani masanin lafiyar jijiyoyin jiki a Jami’ar Calgary.

Hawan jini shine matsalar da aka fi samu yayin da mace take da wanda ke kara matsalar juna biyu har da wajen kashi biyu zuwa uku a cikin dari. Zai iya kawo hadura da yawa wadanda suka hada da hana jini zuwa cikin mahaifa ko haihuwa kafin lokaci.

Ana sa ido ga mata sosai lokacin da suke da juna biyu domin lura da chanji na yadda jininsu ke bugawa, sai dai har yanzu babu wata hanyar da za’a iya tantance yiwuwa ko kuma rigakafin wannan lokacin da matar ke da ciki.

Dr. Ganesh ya kara cewa, wadannan matan suna bukatar lura sosai domin tashin hawan jini, karin maiko a jinni da kuma karin yawan suga ko wadansu yanayoyi da ke iya kai ga shanyewar sashin jiki.

Ba a iya gano ainihin dalilin dake kawo hawan jini yayin juna biyu ba, sai dai wani tunani na nuna cewa yanayin wadansu mata ya sa su a hatsarin kamuwa da hawan jinni fiye da wadansu kuma juna biyu yakan taso da hawan jinin. Ko da yake yana yiwuwa hawan jinin ya sauka bayan haihuwa, ana bukatar a sa ido a kan irin wadannan matan domin a tabbatas da yadda jininsu yake bugawa a kuma yi maganin shanyewar sashin jiki a nan gaba.

“Hawan jini shine hatsari mafi muhimmanci idan ana maganar shanyewar sashen jiki” inji Dr Micheal Hill. “Sanin yadda jininka ke bugawa yana iya zama daya daga cikin muhimman matakai da zaka iya dauka domin rage hatsarin shanyewar shashen jiki, wani abu da yake muhimmi musamman ga matan da suke da tarihin juna biyun da ke da dangantaka da hawan jinni.”

“Yana da muhimmanci mata su san yadda jinin su ke bugawa da kuma irin canjin da wannan zai iya samu a lokacin da suke da juna biyu,” in ji Ian Joiner, daraktan shanyewar jiki dake a gidauniyar zuciya da shanyewar jiki.

“Karuwar bugawar jini na nuna cewa suna bukata suyi magana da likitansu game da hatsarin da ya shafi bugawar jininsu. Babban abin dai shine, matan da ke da hawan jinin dake da dangantaka da juna biyu na bukatar su yi ta gwada bugawar jinin su lokaci lokaci har tsawon rayuwarsu.”