Mata Masu Ciki 60,000 Suke Mutuwa Kowacce Shekara

Mata masu ciki

Bincike ya nuna cewa kimanin mata masu ciki dubu sitiin ne suke mutuwa kowacce shekara domin rashin kulawa.
Bincike ya nuna cewa kimanin mata masu ciki dubu sitiin ne suke mutuwa kowacce shekara domin rashin kulawa.

Kwamishinan lafiya na jihar kwara, Mr. Kayode Issa ne ya bayyana haka a wajen wani taron karawa juna sani da ma’aikatar lafiyar ta shirya akan zubda jini da rage mutuwa wanda aka ba lakabi, ‘Haihuwar Uwa cikin lafiya’.

Kwamishinan ya bayyana cewa, kimanin kashi 59 na matan Nigeriya suke haihuwa ba tare da zuwa awo ba. Bisa ga cewar kwamishinan yana da muhimmanci a inganta kula da mata lokacin haihuwa domin rage mutuwa.

Kwamishina Issa yace kashi 75 cikin 100 na masu da suka sami kula lokacin da suke da ciki zasu haihuwa lafiya daga cikin sauran ashirin da biyar din kuma yana yiwuwa a yiwa guda biyar aiki, daganan kuma 15 zasu samu damuwa.

Saboda haka ya kara karfafa bukatar ganin mata sun je awo domin yana da wuya a iya gane wadanda zasu samu damuwa, da kuma wadanda za’a yiwa aiki har sai ranar haihuwa. Dalili ken an da gwamnatin jihar take bada kudi wajen kula da lafiyar mata masu ciki tana kuma basu magani da yi masu jinya kyauta ta kuma kawo kayayyaki wanda za a rarraba kyauta ga mata masu ciki masu zuwa gwaji.