WASHINGTON D.C —
Wata mace mai kamar maza, ta bayyanawa dandalinvoa cewar karatun boko yayi mata rana a rayuwa domin kuwa a cewarta da shi take takama wajan kulawa da iyalinta inji malama Bilkisu Umar Zandam.
Kamar yadda masu iya Magana suka ce, “tafiya sannu sannu kwana nesa”, malama Bilkisu, ta yi karatu yayin da take fama da dawainiya da iyali amma hakan bai sa tayi kasa a gwiwa ba.
Malama Bilkisu ta ce ko yanzu burinta ya cika dominkuwa sakamakon ilimin da ta samu, yanzu haka ita malama ce a jami’ar Bayero dake jihar Kano, kuma tana cin moriyar karatun wajan kula da iyalinta.
Daga karshe ta kalubalanci mata da basu shawarar tashi su jajirce wajan neman ilimi, da kuma hanyoyin dogaro da kai.
Your browser doesn’t support HTML5